A Nasty Boy
A Nasty Boy Mujallar kwalliya ce ta Najeriya wacce aka kafa a ranar 19 ga Fabrairu, 2017. Ita ce Mujallar LGBTQ ta farko a Najeriya. Littafin ya wallafa labari don murna da labarain mutane, da muryoyin al'ummar LGBTQ da aka ware a Najeriya. Richard Akuson, lauya ɗan Najeriya, ɗan jarida, marubuci, edita, kuma shugaban zartarwa na PR ne ya kafa mujallar sa A Nasty Boy. A watan Yunin 2017, an bayyana mujallar A Nasty Boy a cikin labaran CNN.[1] wanda aka ƙaddamar zuwa sassan duniya. Ba da dadewa ba, Dazed ya ayyana littafin a matsayin mujalla da zai janyo rigima a Najeriya,[2] editocin mujallarVogue sun jero A Nasty Boy a cikin jerin abun karantawa na wannan karon, kamar yadda editocin Vogue suka zaɓo.[3] Mujallar ta sha martabawa daga The Guardian,[4] BBC,[5] France24's The Observers,[6] 1843 Magazine,[7] iD,[8] OkayAfrica,[9] Mic,[10] da dai sauransu. AyyukaGasar Dabarun Don shirin "LGBT pride" na 2017, A Nasty Boy tare da hadin gwiwar WeTransfer, da kuma cibiyar sadarwa, The Dots don nuna tsararraki na gaba na kazakan LGBTQ da suke wanzuwa a duniya.[11] Jerin Nasty 40 A shekara ta 2018, don jerin ƙaddamarwa na A Nasty Boy, mujallar ta ba da haske ga hazakai guda 40 waɗanda ke lalata al'ada ta hanyar fasaha, daukar hoto, rubutu da makamantansu. Jerin ya ƙunshi masu fasaha irin su Ruth Ossai, Adebayo Oke Lawal, Papa Oppong, Yagazie Emezi, da kuma Rich Mnisi.[12] Sabon Shugabanci A watan Janairun 2020, wanda ya kafa shirin wato Richard Akuson ya ba da sanarwar cewa Vincent Desmond zai maye gurbinsa a matsayin sabon edita kuma mawallafin mujallar.[13] Manazarta
Information related to A Nasty Boy |
Portal di Ensiklopedia Dunia