Hari a Buni Yadi, Mayu 2014
Harin Buni Yadi na watan Mayun 2014 wani harin ta'addanci ne da ya faru a ranar 27 ga watan Mayun 2014 a garin Buni Yadi na jihar Yobe a Najeriya.[1][2] An kashe wasu jami'an tsaro 49 (sojoji da ƴan sanda),da fararen hula 9.[3][4][5] An ɗora alhakin kai harin akan ƴan kungiyar Boko Haram.[6][7] MasomiRikicin Boko Haram na tada ƙayar baya, daga ƙungiyar ta Boko Haram. Ya soma ne a shekara ta 2009 a kan gwamnatin Najeriya, amma ya faɗaɗa zuwa kai hari ga wasu jihohi.[8] Kai hariKafin kai harin, mahara da dama ne suka taru a wajen garin da sukayi badda kama cikin wata mota ƙirar Toyota Hilux ɗauke da bama -bamai haɗi da makaman roka. Da misalin karfe 8:00 na UTC, ƴan ta'addan sun kai hari a wani shingen binciken sojoji, inda suka yi ta harbe-harbe kan sojojin da ke wurin. Sannan kuma sun kona ofishin ‘yan sandan yankin tare da kashe ‘yan sandan ciki har da jami’in ‘yan sandan shiyya. An kuma kona wasu gine-ginen gwamnati da dama tare da gidan wani shugaban karamar hukumar. Mayakan sun kai farmaki kan wata makarantar firamare da babu kowa. A cewar wani ganau, maharan sun nufi jami’an tsaro ne, maimakon farar hula. Mutuwar farar hula ta zama kamar ba da gangan ba. An kawo karshen harin da misalin karfe 9:00 a agogon UTC.[1][3] Manazarta
Information related to Hari a Buni Yadi, Mayu 2014 |
Portal di Ensiklopedia Dunia