Juyin mulkin Nijeriya na 1966 ya fara ne a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, lokacin da wasu ƴan ta’addan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Chukwuma Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna suka kashe mutane 22[1] da suka haɗa ciki har da firaministan Najeriya na farko, manyan ƴan siyasa da dama, da manyan hafsoshin Soja (ciki har da matansu), da kuma ma'aikatan da ke aikin basu kariya.[2][3] Masu yunƙurin juyin mulkin sun kai hari a biranen; Kaduna, Ibadan, da Legas, yayin da kuma suka tare kogin Neja da Benue a cikin kwanaki biyu kafin a murƙushe masu yunƙurin yin juyin mulkin. Babban hafsan rundunar sojin Najeriya, Johnson Aguiyi-Ironsi, ya tilasta karɓe ikon mulkin wata ƙasa a cikin ruɗani, ba da gangan ba, wanda ya sanya dimokuradiyyar Najeriya ta koma baya.[4] Hawan sa kan ƙaragar mulki dai, an yi zargin cewa masu yunƙurin juyin mulkin ne, wadanda galibin jami’an ƙabilar Ibo ne, domin share wa Janar Aguiyi-Ironsi hanyar zama shugaban ƙasar Nijeriya. Sakamakon haka, harin ramuwar gayya da ƴan Arewa na Sojojin Najeriya suka yi wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin ƙabilar Ibo da dama da ba su ji ba ba su gani ba, hakan yayi silar haddasa yaƙin basasar Najeriya .[ana buƙatar hujja]
Kafin nan
A watan Agustan shekarata 1965 wasu manyan hafsoshin Soja ( Emmanuel Ifeajuna, Timothy Onwuatuegwu, Chris Anuforo, Don Okafor, Humphrey Chukwuka, da Adewale Ademoyega ) suka fara yunƙurin juyin mulki akan firayim minista na farko kuma mai ci Abubakar Ɓalewa.[5] An cewar Manjo, an dai shirya juyin mulkin ne saboda mutanen da ke riƙe da madafun iko sun yi wa Najeriya ɓarna ta gurbatattun hanyoyinsu. Ministocin da ke ƙarƙashin su, sun kasance suna rayuwa mai daɗi da wawushe dukiyar al’umma, suna kashe talakawan ƙasa.[ana buƙatar hujja]
Shugaban Najeriya Nnamdi Azikiwe ya bar ƙasar ne a karshen shekarar 1965, inda ya fara tafiya zuwa Turai, sannan ya yi balaguro zuwa yankin Caribbean. A ƙarƙashin dokar, shugaban majalisar dattijai, Nwafor Orizu, ya zama shugaban riƙo a lokacin... da ba ya nan kuma ya karɓe dukkan ikon ofishin.[6]
Juyin mulki
Da safiyar ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, a wani taro da wasu ƴan jarida na cikin gida, suka yi a Kaduna don neman sanin abin da ke faruwa, an kawo wa Manjo Nzeogwu cewa kawai bayanin abubuwan da suka faru a lokacin shi ne abin da BBC ke haɗawa.[5] Nzeogwu ya yi mamaki domin ya yi tsammanin za a watsa rahoton bayanan rediyon ƴan tawayen daga Legas. An ce ya ɗimauce a lokacin da ya samu labarin cewa Emmanuel Ifeajuna a Legas bai yi wani shiri ko kaɗan ba don kashe Johnson Aguiyi-Ironsi wanda shi ne Kwamandan Sojoji. Don haka Nzeogwu ya yi gaggawar shirya jawabin da aka watsa a gidan rediyon Kaduna da misalin karfe 12 na safe inda ya ayyana dokar ta-ɓaci a kan lardunan Arewacin Najeriya.[7][8]
Bayan haka
Muƙaddashin shugaban ƙasar Nwafor Orizu ya yi wani jawabi a faɗin ƙasar, bayan da ya yi wa shugaban ƙasar Nnamdi Azikiwe bayani ta wayar tarho game da matakin da majalisar ministocin ta ɗauka, inda ya bayyana matakin da majalisar ta ɗauka na miƙa mulki ga sojojin ƙasar.[ana buƙatar hujja] Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya yi nasa watsa shirye-shirye, yana karɓar "gayyatar". A ranar 17 ga watan Janairu, Manjo Janar Ironsi ya kafa Majalisar Koli ta Sojoji a Legas kuma ya dakatar da tsarin mulki yadda ya kamata.[9]
Abubuwan da suka faru
Dangane da irin hasarar da aka yi, masu yunƙurin juyin mulkin sun yi iƙirarin kawar da su bayan juyin mulkin da aka yi wa ƴan uwa ko magoya bayan gwamnatin baya, kuma an kai su ne don dalilai na siyasa kawai maimakon zama kawar da ƙabilanci da aka mayar da hankali kan wata ƙabila ko kabilu; Bugu da ƙari, sun kuma yi iƙirarin cewa jerin mutanen da suke neman kai wa hari, basu da yawa, waɗanda suka kunshi mutane 8 ne kacal, rabinsu daga cikin su, ƴan kasashen waje ne da ake shirin kamawa ba a kashe su ba, kuma waɗanda aka kashe din hakan ya faru ne a yayin yunƙurin juyin mulkin. Wadannan iƙirari sun fito ne daga wani memba na mutanen uku da suka yi juyin mulki, Adewale Ademoyega, wanda aka wallafa/buga (iƙirarin) a Najeriya a cikin shekara ta 1981 a cikin wani littafi mai suna Me Ya Sa Muka Buƙaci, littafin ya littafin ya bayyana dalilansu da burikan su[10] inda ya zayyano:
" Babu wata shawara a taronmu na ware wata ƙabila domin kawar da ita. Burinmu abin alfahari ne, ra'ayoyinmu na ƙasa ne, haka-zalika burinmu na da manufa. Hatta waɗanda aka ware domin a kamosu, huɗu daga cikin su, ƴan Arewa ne, biyu daga yankin Yamma, biyu kuma daga Gabashin ƙasar suka fito. "
A ƙasa akwai cikakken jerin sunayen waɗanda suka mutu a yayin tarzomar juyin mulkin.[1]
Sajan Daramola Oyegoke (ya taimaka wa Nzeogwu a harin da aka kai a masaukin Sardauna kuma a cewar rahoton ƴan sanda Nzeogwu ne ya kashe shi)[2][3]
PC Yohana Garkawa
Lance Kofur Musa Nimzo
PC Akpan Anduka
PC Hagai Lai
Philip Lewande
Manazarta
↑ 1.01.1Siollun, Max (2009). Oil, Politics and Violence: Nigeria's Military Coup Culture (1966-1976). Algora Publishing, 2009. p. 237. ISBN9780875867106.